Ban janye kudurin neman takarata ba ta 2023 – Tinubu ga gwamnonin APC

0 66

Jagoran Jam’iyar APC na Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Gwamnonin Jam’iyar APC a yau da safe a birnin tarayya Abuja.

An gudanar da zaman ne a Gidan Gwamnan Jihar Kebbi da ke Asokoro a Abuja, awanni Kalilan da mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya ayyana kudurin sa na tsayawa takarar shugabancin Kasa a karkashin tutar Jam’iyar APC.

Chief Bola Tinubu, na daga cikin mutanen da suke neman kujerar shugabancin kasa karkashin tutar Jam’iyar APC.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci ganawar sun hada da Gwamnan Jihar Kebbi kuma shugaban Kungiyar Gwamnonin APC Atiku Bagudu, da Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, da Osun Gboyega Oyetola, da na Legas Babajide Sanwo-Olu, da Gwamnan Plateau Simon Lalong da kuma na Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i.

A jiye ne Osinbajo ya gana da Gwamnonin APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kafin ya bayyana kudurinsa na neman takara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: