Ma’aikatar Wutar Lantarki ta kasar ta ce tana gudanar da bincike kan lalacewar wutar lantarki da ake samu a kasar nan

Wannan na zuwa ne bayan kara samun lalacewar wutar a ranar Juma’a a karo na uku cikin makonni da dama, lamarin da ya jefa sassan kasar cikin duhu.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce tuni aka fara aikin dawo da martabar ma’aikatar.

Maa’ikatar ta ci gaba da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan musabbabin faduwar wutar lantarki da hukumar kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya ta gudanar.

Kuma ana ci gaba da gudanar da aikin dawo da kayan aiki tare da samar da wadattacciyar wutar lantarki.

Ta kuma tabbbatar wa ‘yan Najeriya cewa, Gwamnatin Tarayya na aiki tukuru don ganin an aiwatar da gyare-gyare da saka hannun jari da ake bukata a fannin wuta.

Wadanda ke da matukar muhimmanci wajen inganta hada-hadar kudi a fadin kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: