Bisa kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na baya-bayan nan an kashe fararen hula dubu 1 da 207 tun bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine

0 104

Bisa kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na baya-bayan nan, an kashe fararen hula dubu 1 da 207 tun bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Kakakin hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Liz Throssell ta ce adadin ya hada da mutane 406 da aka kashe sannan wasu 801 suka jikkata amma akwai yiyuwar alkaluman su zarce haka.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma bayyana damuwarta kan yadda ake tsare da magoya bayan Ukraine ba bisa ka’ida ba a yankunan da ke karkashin ikon sojojin Rasha, da kuma cin zarafin da ake yi wa masu ra’ayin Rasha a yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin Ukraine.

Alkaluma na baya-bayan nan na Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa an kama wasu mutane dubu 12 da 700 a Rasha saboda gudanar da zanga-zangar lumana ta adawa da yaki.

Majalisar ta dinkin duniya ta soki dokokin danniya da Rasha ta kakaba a baya-bayan nan da suka sanya hukuncin daurin shekaru 15 a kan wadanda ake tuhuma da yada labaran karya game da mamayar, ko kuma bata sunan sojojin Rasha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: