Yan fashin daji sun saki dagacin Kauyen Guga a yankin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina bayan sun karbi diyyar naira miliyan 28

0 77

‘Yan fashin daji sun saki dagacin Kauyen Guga a yankin karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, Alhaji Umar, tare da sauran wasu mutanen kauyen su 35, bayan sun karbi diyyar naira miliyan 28.

Mutanen da aka sace sun kwashe kwanaki 29 a hannun masu garkuwa da su kafin daga bisani a sake su a ranar Lahadi.

Babban dan dagacin da sirikinsa ne suka tabbatar da sakin dagacin a jiya da dare.

A cewar sirikinsa, Nafi’u Muhammad, ‘yan fashin dajin sun kira iyalansa a waya kwanaki 2 bayan sace mutanen, inda suka nemi kudin fansa.

Babban dan sa mai suna Abdullahi Umar, yace wadanda aka saki sun dawo kyauyen Guga cikin dare inda ma’aikatan lafiya daga karamar hukumar Bakori suka duba su.

Da aka tambayeshi akan yadda suka hada naira miliyan 26, Abdullahi Umar yace sun sayar da dukkan abubuwan da suka mallaka kuma sun nemi tallafin wasu masu hannu da shuni a jihar.

Ya kara da cewa an nemi kowa da kowa a garin ya bayar da gudunmawa, ciki har da wadanda basu da alaka da mutanen da aka sace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: