Matafiya 7 sun mutu a wani hadarin mota akan titin Suleja zuwa Minna a jihar Neja

0 86

Matafiya 7 sun mutu a wani hadarin mota akan titin Suleja zuwa Minna a jihar Neja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Wasiu Abiodun yace hadarin da ya rutsa da wata mota kirar bus, ya auku da misalin karfe 7 na yammacin jiya a Kauyen Farin-Doki dake yankin karamar hukumar Paikoro ta jihar.

Ya kara da cewa motar ta taso daga Katsina tana tafiya zuwa Lagos lokacin da sitiyarin Motar ya kwacewa direbanta a kauyen Farin-Doki.

Yace tawagar ‘yansandan sitiri dake aiki da ofishin ‘yansanda na Paiko sun gaggauta zuwa wajen da hadarin ya auku, inda suka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin duba lafiyarsu, yayin da suka ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawarwaki a asibitin kwararru na Ibrahim Babadamasi Babangida.

Wani wanda ya shaida lamarin yace wadanda suka mutu akwai maza 5 da wata mace tare da wani yaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: