Yansanda a jihar Jigawa sun kama wani mutum mai shekaru 46 bisa laifin garkuwa da mutane a karamar hukumar Kirikasamma

0 109

‘Yansanda a jihar Jigawa sun kama wani mutum mai shekaru 46 bisa zargin garkuwa da mutane a yankin karamar hukumar Kirikasamma.

Kakakin ‘yansanda na jiha, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da haka yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa a Dutse.

Yace wanda ake zargin mai suna Adori Ahmadu, ya fito ne daga Kauyen Marawaji a yankin karamar hukumar Kirikasamma.

Shiisu Adam yace wanda ake zargin, an kama shi a ranar 28 ga watan Fabrairu, kuma ana kyautata zaton dan wani gungun ‘yan fashi ne wadanda a ‘yan kwanakinnan suka yi garkuwa da wata mata mai shekaru 22 mai suna Hadiza Alhaji-Chadi a garin Marma dake karamar hukumar.

Shiisu Adam ya kara da cewa an ceto Hadiza Alhaji-Chadi ba tare da ji rauni ba, a daya daga cikin ayyukan ‘yansanda, bayan sun kai farmaki wurin da ake zargin maboyar masu garkuwa da mutane ce a yankin karamar hukumar Suletankarkar.

Yace ana cigaba da bincike kan lamarin har ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton.

Leave a Reply

%d bloggers like this: