Shugaban kasa Bola Tinubu yace gwamnatin sa ta himmatu matuka wajen wadata kasar nan da abinci ta yanyar bunkasa ayyukan noma, domin ganin ta tsaya da kafarta wajen samar da abinci, har ma ta samu rarar da za ta iya fitar da ita kasashen ketare.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne lokacin da yake karɓar baƙuncin shugabannin Ɗariƙar Tijjaniya na duniya wanda Khalifa Muhammad Mahe Niass, ya jagoranta.
Yayin ganawar shugaban kasar ya ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin Shugabannin addini da na siyasa wajen ciyar da ƙasa gaba.
Tinubu ya ce gwamnatinsa a shirye take wajen ciyar da harkokin addini ga wadanda suke taimakawa wajen gina ƙasa.
Da yake nasa jawabin a madadin wakilcin masu ziyarar Khalifa Muhammad Mahe Niass ya yaba wa Gwamnatin Tinubu wajen ƙoƙarin da take yi na ganin an samu zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya. Yayin ziyarar tawagar ta yi addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a kasa da nahiyar Afrika dama duniya baki ɗaya.