Kamata yayi a zargi Janar Muhammadu Buhari kan yadda ya mulki Najeriya – Muhammadu Sanusi

0 237

Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN Muhammadu Sanusi yace maimakon yan najeriya su rika dora alhakin matsin tattalin arzikin da ake fuskanta, kamata yayi a zargi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya mulki kasar.

Tsohon gwamnan na Kano wanda yayi magana a wani taron maulidi a Abuja, ya dora alhakin gazawa wajen daidaita tattalin arzikin kasa ga gwamnatin data gabata.

A cewar sa, Buhari yayi kunnen kashi ga shawarwarin da kwararru suka bashi dangane da mafitar kasar a turbar tattalin arziki.

Yace ya kasa cimma tsammani da muradan yan kasa da suke cigaba da kalubalantar shugaba Tinubu kan wahalhalun da aka shiga a kasa. Sunusi yace mawuyacin halin da yan Najeriya ke fuskanta somin tabi ne kawai, idan ba’a dauki matakan da suka dace ba, domin a cewar sa Najeriya ba zata iya kaucewa makamancin lamuran da suka faru a kasashen Jamus, Zimbabwe, Uganda da Venezuela ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: