Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kwace kwalaben barasa akalla 8,600

0 137

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kwace kwalaben barasa akalla dubu takwas da dari shida da aka loda cikin wata mota da ta shiga jihar daga Kaduna.

Jami’in hukumar da ke yaki da kayan maye, Idris Ibrahim wanda ya bayyana haka ga yan jarida a karshen mako, ya ce an kwace barasar ne ranar Alhamis a kauyen Kwanar Dangora da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Kaduna.

Jaridar Vanguard ta ruwaito jami’in na bayyana cewa jami’an Hisbah sun yi ta bibiyar motar daga Kaduna har ta isa Kano.

Ibrahim ya kara da cewa tawagar hukumar da ke yaki da kayan maye suna dakon umarni daga manyan jami’an Hisbah.

A cewarsa, Hisbah ta kuma kama yan mata 15 masu zaman kansu a wurare daban-daban na jihar Kano.

Bayanai na cewa an kama matan ne a unguwannin Hotoro da Tishama da Sabon Gari da titin Miyangu da titin Hadeja da kuma tsohuwar tashar mota da ke Titin Zoo Road. Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dr Mujahid Aminuddeen wanda ya tabbatar da kamen ya ce an sha kama wasu daga cikin wadanda ake zargi masu zaman kansu ne inda aka gurfanar da su gaban kotu amma sun ci gaba da aikata haramtacciyar sana’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: