Ma’aikatan gwamnatin tarayya sun karbi albashin su na watan junairu

0 237

Gwamnatin tarayya tace dukkan ma’aikatan ta daga ma’aikatu da sassa da cibiyoyin gwamnati 90 sun karbi albashin su na watan junairu.

Ofishin shugaban ma’aikata na kasa da shugabannin wasu hakumomi sun sanar da manema labarai cewa sun gana da abokanan aikin su, sun kuma tabbatar da cewa sun amshi albashinsu na watan junairun.

Haka kuma daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Bawa Mokwa, ya sanar da cewa  suna sane da cigaban da aka samu daga dukkan ma’aikatan hakumomin gwamnati na jinkirin albashin.

Amma ya bayyana cewa irin wannan jinkiri ba zai sake faruwa ba a nan gaba. A daren ranar lahdin data gabata yace cikin wadanda jinkirin ya shafa har da ma’aikatan wasu jami’o’I da kwalejojin kere-kere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: