Gwamnonin jam’iyyar PDP sun jaddada matsayinsu kan aikin ‘yan sandan jihohi

0 206

Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, sun jaddada matsayinsu kan aikin ‘yan sandan jihohi, a matsayin mafita ga tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Gwamnonin ‘yan adawar sun kuma yi tir da faduwar Naira a kyauta da sakamakon da ke tattare da ita, kuma sun nemi kungiyar tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya ta samar da hanyoyin da suka dace don magance kalubalen.

Shugaban kungiyar, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyanawa manema labarai bayan taron gwamnonin a Abuja.

Ya koka kan tsadar rayuwa a kasar, da kuma faduwar darajar Naira, yana mai cewa, Najeriya ta kama hanyar zamowa tamkar Venezuela, kasar da ke fuskantar matsananciyar matsalar tattalin arziki da tsaro.

Taron wanda ya samu halartar gwamnonin jam’iyyar da suka hada gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da  Seyi Makinde naOyo, Ahmadu Fintiri na Adamawa, Caleb Mutfwang na Plateau, Dauda Lawal na Zamfara, Kefas Agbu naTaraba da kuma gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: