Uwargidan shugaban kasar da ta kaddamar da ginin da aka sanyawa sunanta a jami’ar MAAUN ta Kano

0 217

Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Tinubu ta sanar da bayar da tallafin naira miliyan 50 ga daliban da suka kammala karatun lauya a jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria, MAAUN, Kano.

Misis Tinubu ta bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da Makarantar Koyon Aikin Shari’a da Hukumar Jami’ar ta sanya mata suna.

Uwargidan shugaban kasar da ta kaddamar da ginin, ta bayyana gamsuwarta da kayyakin da aka tanada tare da godewa wanda ya kafa Jami’ar, Farfesa Adamu Gwarzo da ya sanyawa ginin Makarantar sunanta.

Ta kuma yabawa Gwarzo bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen daukaka darajar ilimi a Najeriya da ma sauran kasashen duniya.

Misis Tinubu ta bayyana cewa ta yi aikin hidimtawa kasa na shekara daya NYSC ta kuma zauna a unguwar Sabon Gari da ke cikin Birnin Kano.

Tun da farko, Gwarzo ya ce manufar MAAUN ita ce ta zama jami’a mai daraja ta duniya wacce ta shahara a fannin koyarwa, bincike da kuma hidima ga bil’adama a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: