Hakar ma’adanai dake gudana a Najeriya sun tallafa matuka wajan karuwar matsalolin tsaro

0 267

Mataimakin kakakin majalisar wakilai ta kasa Benjamin Kalu, yace ayyukan hakar ma’adanai dake gudana a Najeriya sun tallafa matuka wajan karuwar matsalolin tsaro da kasar ke fama da ita.

Mataimakin kakakin majalisar ya bayyana haka ne a Abuja a wani taron ganawa na kwamatin ma’adanai na majalsar wakilai.

Taron ganawar wanda ya tattara dukkan kwararru, da masu ruwa da tsaki a fannin hakar ma’adanai ya gudana ne domin bunkasa fannin cigaban zamantakewa da tattalin arziki a kasa.

Benjamin Kalu ya bayar da tabbacin cewa ma’adanan karkashin kasa sun kasance wadanda ba’a amfana da su, yana mai cewa majalisa ta 10 tana aiki domin cigaban fannin.

Mataimakin Kakakin yayi bayanin cewa fannin idan ya inganta zai bunkasa harkokin samar da ayyukan yi ga miliyoyin yan Najeriya tare da habaka ma’aunin tattalin arzikin kasa na GDP.

Haka kuma gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, wanda ya kasance daga cikin mahalarta taron yace domin cimma muradun da aka sanya a gaba game da fannin, akwai bukatar sake jaddadawa da nazartar wasu ka’idojin a fannin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: