Burkina Faso ta dakatar da wasu kafafen watsa labarai da dama na Ƙasashen Yamma har sai baba ta gani

0 99

Burkina Faso ta dakatar da waɗansu daga cikinsuda kafafen watsa labarai da dama na Ƙasashen Yamma har sai baba ta gani.

Daga cikin waɗanda aka dakatar akwai jaridar Faransa ta Le Monde da The Guardian ta Birtaniya da Deutsche Welle ta Jamus da TV5 Monde ta Faransa, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan kafafen watsa labarai ta CSC ta sanar.

An dakatar da su ne sakamakon wani rahoto da suka bayar na ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch wadda ya zargi sojojin da kai hari kan fararen hula a yaƙin da sojojin ke yi da masu tayar da ƙayar baya.

Sauran kafafen watsa labaran da aka dakatar a sanarwar baya-bayan nan sun haɗa da jaridar Ouest-France da APAnews da Agence Ecofin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: