CBN Ta Ba Bankuna Umarnin Kulle Asusun Mutanen da Ake Zargi da Alaƙa da Ta’addanci

0 76

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci dukkan bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi da su gaggauta daskarar da asusun mutanen da hukumomi suka sanya cikin jerin masu alaƙa da tallafa wa ayyukan ta’addanci.

A cikin wata sanarwa da Olubunmi Ayodele-Oni ya sanya wa hannu a madadin CBN, bankin ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan sabbin sunayen da Kwamitin Takunkumin Najeriya da kuma Ofishin Kula da Kadarorin Ƙasashen Waje na Ma’aikatar Kuɗin Amurka (OFAC) suka fitar.

Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta sanya wa wasu mutane uku da kamfanoni shida takunkumi bisa zargin taimakawa wajen samar da kuɗaɗen ayyukan ƙungiyar ISIS, ciki har da wasu kamfanonin canjin kuɗi (BDC) na Najeriya guda uku.

Daga cikin waɗanda aka ambata akwai Mukhtar Adamu Muhammad, wanda ake zargin yana da hannu wajen samar da kuɗaɗen ayyukan ISIS a Turai, Gabas ta Tsakiya da kuma Yammacin Afirka.

Kamfanonin Najeriya da aka sanya cikin jerin sun haɗa da Generation Currency Bureau De Change Limited da ke Legas, Manhattan Bureau De Change Limited da ke Kano, da kuma Nine to Nine Exchange Bureau De Change Limited da ke Legas.

CBN ya umarci cibiyoyin kuɗi da su daskarar da duk wasu kuɗaɗe, kadarori ko albarkatun tattalin arziki da ke hannun waɗannan mutane ko kamfanoni, kai tsaye ko a kaikaice, ba tare da sanar da su ba.

Haka kuma, bankin ya buƙaci bankuna su binciki bayanan kwastomominsu da mu’amalolinsu domin tabbatar da cewa babu wata alaƙa da sunayen da aka sanya wa takunkumi.

CBN ya kuma haramta samar da duk wata hidimar kuɗi ko wata hanya da za ta anfani waɗannan mutane ko kamfanoni.

Sannan ya umurci cibiyoyin kuɗi da su kai rahoton duk wata mu’amala mai tayar da zargi ga Hukumar Binciken Bayanai Kan Kuɗi ta Najeriya (NFIU), tare da gabatar da cikakken rahoto ga CBN cikin sa’o’i 48 idan an gano wata alaƙa.

Babban bankin ya gargadi bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi cewa duk wanda ya gaza bin wannan umarni zai fuskanci hukunci bisa dokar BOFIA ta 2020 da sauran dokokin da suka dace.

CBN ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da sa ido da gudanar da bincike domin tabbatar da cewa an bi umarnin yadda ya kamata a faɗin ƙasar.

Leave a Reply