CBN ya gargadi jama’a da kada su yi dinga wulakanta kudin naira

0 196

Babban bankin Najeriya (CBN) ya gargadi jama’a da kada su yi dinga wulakanta kudin naira.

Babban bankin ya tabbatar wa al’umma cewa zai yi kokari wajen ganin an samu kudaden da za a yi mu’amalar cinikayya da su.

Daraktan Sashen Sadarwa na Babban Bankin, Dakta Isa Abdulmumin shi ne ya bayyana hakan a Lokoja jiya a yayin bikin baje kolin na CBN da aka gudanar a babban birnin jihar.

Ya kuma bukaci jama’a da su rika ganin Naira a matsayin babbar alama ta kasa, yana mai jaddada cewa wajibi ne a gare su su mutunta tare da tsaftace ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: