Gwamnatin Tarayya zata aiwatar da tsarin babu aiki, babu biyan albashi ga mambobin kungiyar likitocin masu neman kwarewa da ke yajin aiki

0 191

Gwamnatin Tarayya ta umurci manyan Daraktocin Likitoci a manyan asibitocin gwamnatin tarayya da su aiwatar da aikin babu aiki, babu biyan albashi ga mambobin kungiyar likitocin masu neman kwarewa da ke yajin aiki.

Haka nan gwamnatin ta kuma umurci asibitocin da su kula da rijistar halartar zuwa wuraren aiki ga duk likitocin da ke son yin aiki.

Ma’aikatar lafiya ta tarayya ce ta rubuta wasikar da wakilinmu ya samu a jiya, kuma ta aike zuwa ga ma’aikatan na daukacin Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke fadin kasar nan.

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta shiga yajin aiki tun a ranar 26 ga Yuli, 2023, kan neman a biya mata wasu bukatunta. Yajin aikin ya biyo bayan cikar wa’adin makonni biyu da kungiyar ta baiwa gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: