Cibiyar horas da malaman makaranta ta ƙasa (NTI) tana aikin horas da malaman makaranta 925

0 248

Cibiyar horas da malaman makaranta ta kasa (NTI) da ke Kaduna tana aikin horas da malaman makaranta 925 akan fannoni masu muhimmanci a taron karawa juna sani na malamai a karkashin shirin dorewar manufofin cigaba.

Ana gudanar da aikin bayar da horon a fadin jihoshi 36 da babban birnin tarayya.

Shugaban cibiyar, Musa Maitafsir, cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana bayar da muhimmanci akan samar da ilimi mai inganci ga ‘yan kasa.

A jawabin da ya aikawa mahalarta horon a dukkanin cibiyoyin bayar da horon, Maitafsir ya yabawa gwamnati mai ci bisa sakin kudaden gudanar da taron karawa juna sani na bana.

Maitafsir yace ana gudanar da taron karawa juna sani da nufin saukakawa masu bayar da horon a cibiyoyin bayar da horon.

Daga nan sai ya roki dukkan mahalartan da su rungumi sabon tsarin saboda a samu canjin da ake bukata a aikin bayar da horon.

Leave a Reply

%d bloggers like this: