Cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya dake Birnin Kudu zata gina sabon asibiti domin kara inganta harkokin kiwon lafiyar alumma

0 105

Cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya dake Birnin Kudu, zata gina sabon asibiti domin kara inganta harkokin kiwon lafiyar alumma.

Babban Likitan Asibitin, Dr Adamu Abdullahi Atawami, ya sanarda hakan ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Yace gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa cibiyar fili tun shekarar 2016 domin gina sabon asibiti da nufin kara samar da ofishi da cibiyoyin kula da lafiya dana bincike.

Dr Adamu Abdullahi yace suna da yakinin cewa da zarar an kammala ginin sabon asibiti nan da shekaru biyu masu zuwa, zasu mayar da tsohan asibitin zuwa makarantar koyan aikin jinya da kuma kiwon lafiya.

Ya kara da cewa za a gina cibiyar kula da masu cutar cancer a cibiyar, domin ganin marasa lafiya masu cutar sun daina zuwa Gombe da Zaria domin neman magani.

Babban Likitan Asibitin yace ya yi tattaki zuwa birnin Abuja tare da samun karin aiyuka da za a gudanar a asibitin domin kara inganta aiyukan kula da lafiyar jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: