Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga yanzu ta dakatar da bayar da takardar wucin gadi ta mallakar filaye

0 58

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga yanzu ta dakatar da bayar da takardar wucin gadi ta mallakar filaye.

Kwamishinan ma’aikatar kasa da safiyo, Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka lokacin da shugabanin kungiyar dillalan filaye da bada gidajen haya na jihar jigawa suka ziyarci ofishinsa.

Sagir Musa Ahmed ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne da nufin kawar da irin matsalolin da ake fuskanta ta fuskar bada filaye fiye da sau daya.

Ya ce gwamna Muhammad Badaru, ya amincewa ma’aikatar fara amfani da tsarin tattara bayanan taswirar filaye da gidaje ta kafar sadarwar zamani nan bada jimawa ba.

Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnati na yin aiki da yan kungiyoyi domin cimma burin da aka sanya a gaba ta fuskar filaye da gina gidaje.

A jawabinsa, shugaban kungiyar dillan filaye da bada hayar gidaje na jiha, Malam Garzali Yalwawa ya ce sun kawo ziyarar ne domin gabatar da bukatu da matsalolin da kungiyar take fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: