Wata kotun shari’ar musulunchi a Kano ta bayar da umarnin cigaba da tsare wani mutum saboda satar katan-katan na Maggi
Wata kotun Shari’ar Musulunchi a Kano ta bayar da umarnin cigaba da tsare wani mutum mai shekaru 37 mai suna Yusha’u Ado, saboda satar katan-katan na Maggi.
Mutumin wanda mazaunin Unguwar Goron Dutse ne dake Kano, yana fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da cin amana da sata.
Wanda ake kara ya amsa laifinsa.
A wani labarin kuma, ‘yansanda a jihar Kano sun kama wasu mutane 3 masu satar dabbobi da suka addabi mazauna kauyen Aujarawa Alkali a yankin karamar hukumar Gezawa.
Kakakin ‘yansanda na jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace bincike ya jawo an kama wanda yake sayen dabbobin da barayin suka sato.