Dalilan da yasa aka kai Jacob Zuma asibiti dake kusa da gidan yari

0 69

An kwantar da tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma a wani asibiti da ke wajen gidan yari domin duba lafiyarsa, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar.

Hukumomin gidan yarin sun ce yana da ƴancin neman magani kamar sauran ƴan gidan yarin da ake tsare da su.

A matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa ana duba lafiyarsa ne a sibitin soji, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Gidauniyarsa ta ce ana duba lafiyarsa ne kamar yadda ya saba duk shekara, inda ta kara da cewa babu buƙatar tayar da hankali.

Tsohon shugaban ƙasar na zaman gidan yari ne na ɗaurin watanni 15 da aka yanke masa tun a ranar 7 ga Yuli.

A mako mai zuwa, tsohon shugaban ake sa ran zai sake gurfana a gaban kotu kan wani zargi na daban da ake masa da ya shafi cinikin makamai da rashawa.

Ya musanta zargin da ake masa da ya shafi kuɗi dala biliyan biyar.

Daurin da aka yi masa ya haddasa tarzoma a kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 300.

Leave a Reply

%d bloggers like this: