Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta kama mutum 2 bisa zargin laifin safarar mutane

0 78

Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta kama mutane 2, bisa zargin su da laifin safarar mutane, tare da kubutar da mutane 14 daga hannun su.

Mutanen da aka kubutar sun fito ne daga jihohi 9 da suke fadin kasar nan, wanda suka kunshi Maza 3 da Mata 11, bayan an biyo dasu ta karamar hukumar Mashi ta jihar Katsinan.

Kakakin rundunar yan sandan JIhar Katsina SP Gambo Isah, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi, inda ya kara da cewa mafiya yawan mutanen da aka kubutar din sun fito ne daga Jihohin kudancin Najeriya, kuma suna son tsallaka zuwa Libya domin tafiya kasashen Italiya, da Spain da kuma nahiyar Turai.

A cewarsa, mafiya aka sarin mutanen da aka yi safarar tasu sun fito ne daga Jihohin Lagos, Ondo, Osun, Ogun, Delta, Anambra, Akwa Ibom, Benue, da kuma jihar Kwara.

Kazalika ya nanata kudurin rundunar na tabbatar da cewa babu mutum daya da aka bari daga cikin masu safarar mutanen, ba tare da an hukunta su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: