Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya koka da halin da Najeriya take ciki

0 78

Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Mohammed Saad Abubakar, ya ce al’amura na ƙara rincaɓewa a Najeriya, yayin da rashin abinci ke haifar da matsalar tsaro.

Mohammed Saad ya bayyana haka ne a Jihar Gombe a ranar Alhamis, yayin taron samar da zaman lafiya na ƙasa da kwamitin Da’awa na Najeriya ya shirya.

Sarkin Musulmin ya ce duk mai jin yunwa a lokuta da dama yakan zama fusatacce a rayuwa.

A cewarsa, Matsalar Najeriya kullum gaba ta ke yi, inda ya ce ka da yan Najeriya su yaudari kansu ta hanyar cewa al’amura na gyaruwa, alhali kuma abubuwa ƙara taɓarɓarewa su ke yi.

Sarkin ya ce abin da ake fuskanta a ƙasar nan shine ba ma gayawa kanmu gaskiya, babu addinin da ya ce a kashe kowa.

Haka kuma ya ce ta’addanci, da sace-sacen mutane, da kuma ‘yan bindiga, sune suke tsayar da kasuwanci a kasa, saboda mutane ba sa iya tafiye-tafiye cikin aminci.

Kazalika, ya ce Mutane da yawa na cikin yunwa, saboda ba za su iya sayan abinci ba, inda ya bukaci a tabbatar da samar da abinci saboda mutanen da suke da rauni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: