Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da tsawaita lokacin sake bude makarantu a Jihar saboda kalubalen tsaro

0 55

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da tsawaita lokacin sake bude makarantu a Jihar saboda kalubalen tsaro.

A baya dai, Jihar ta sanar da ranar tara ga watan Agustan 2021 a matsayin ranar da za a sake bude makarantu don fara sabon zangon karatu na uku.

Sai dai gwamnatin ta ce ayyukan da dakarun soji ke gudanarwa yanzu haka ta sama da kasa kan ’yan bindiga a iyakarta da Jihohin Neja da Katsina da Filato da kuma Zamfara ba za su bari a sake bude makarantun ba.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Shehu Usman Muhammad, da takwaransa na Tsaro da Al’amuran Cikin Gida, Samuel Aruwan, ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwa a jiya Juma’a.

Sun ce Jihar ta kuma umarci jami’an tsaro da su kara zafafa kai hare-hare a sabbin maboyar ’yan bindigar da aka gano a kwanan nan.

Haka kuma sun bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta karbi shawarwarin tsaron da aka bata, kuma a kan haka take umartar dukkan makarantu da su bi wannan umarnin sau da kafa.

Sanarwar ta ce za a sanar da sabuwar ranar sake bude makarantun da zarar al’amuran tsaro sun inganta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: