Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa ta sanar da sabbin mutane 565 da suka kamu da Korona

0 79

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa wato NCDC, ta sanar da sabbin mutane 565 da suka harbu da cutar Corona a jiya Juma’a.

Wannan na nuni da cewa adadin mutanen da suke cigaba da karbar magani a cibiyoyin sun kai dubu 9,000.

Cibiyar NCDC ta ce an samu sabbin mutanen ne a jihohi 6 ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Jihohin sun hada da Lagos (348), Rivers (70), Akwa Ibom (45), Oyo (36), FCT (24), Ekiti (15), Kwara (7), and Ogun (7).

Sauran sune Gombe (3), Anambra (2), Kaduna (2), Bayelsa (1), Cross River (1), Edo (1), Plateau (1), Kano (1), and Sokoto (1).

Haka kuma cibiyar ta sallami mutane 86 da suka warke.

Adadin mutane da cutar Corona ta kashe, kawo yanzu sun kai mutane dubu 2,178.

Adadin mutanen da cutar Corona ta kama ya kai mutane dubu 177,142, sai kuma mutane dubu 165,409 da suka warke daga cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: