Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin ’yan bindiga a Zamfara

0 94

Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin ’yan bindiga da dama bayan wasu jerin hare-hare da suka kai da jiragen yaki a dazukan Jihar Zamfara.

Hare-haren jiragen yakin sun kuma yi sanadiyyar kashe ’yan bindiga akalla 78, kamar yadda wata majiya daga cikin sojojin ta shaida wa kafar yada labarai ta PRNigeria a jiya Juma’a.

A cewar majiyar, “Sashen sojojin sama na rundunar tsaro ta Operation Hadarin Daji ta kai wasu jerin hare-hare kan ’yan bindiga a Jihohin Arewa maso Yamma a cikin kwanaki uku.

A kokarinta na kakkabe yankin daga ayyukan ’yan bindiga, rundunar ta mayar da hankali a kan yankunan da aka fi samun taruwarsu, musamman a dazukan Dansadau da Kuyambana a Jihar ta Zamfara.

Kazalika, sojojin da suka yi aiki ta kasa yayin hare-haren sun tabbatar da kakkabe ragowar ’yan bindigar da ke raye daga dajin.

A wani cigaban kuma, rundunar Sojin Saman Najeriya ta 404, wanda sukayi sansani a Kaduna, sunyi nasarar kama wani mutum mai suna Aminu Saminu mai shekaru 48, bisa zarginsa da kaiwa yan bindiga Makamai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: