Gwamnatin jihar Jigawa ta nanata kudurinta na cike gibin karancin ma’aikata a fannin Lafiya

0 83

Gwamnatin JIhar Jigawa ta nanata kudurinta na cike gibin karancin Ma’aikata a fannin Lafiyar jihar nan.

Kakakin Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, kuma Jami’in hulda da Jama’a a madadin Gwamna, Alhaji Habibu Nuhu Kila, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Dutse.

A cewarsa, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, shine ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake yin bankwana da daliban jihar nan 160, wanda zasu tafi kasar Sudan domin yin karatun Likitanci.

Habibu Kila, ya rawaito gwamna Badaru na cewa gwamnatinsa tana bada fifiko a fannin lafiya, kamar yadda hakan yake cikin kudure-kuduren gwamnatin.

Sanarwar ta ce gwamna Badaru Abubakar ya ce babu wata cibiyar lafiya da zata zama bata da kwararren likita a cikinta.

Haka kuma Gwamnan ya bada tabbacin cewa kowanne gari zai samu cibiyar Lafiya mai inganci.

A shekarar 2016, gwamnatin jihar Jigawa ta tura Daliban da suka kammala Sikandire su 60 domin yin karatun likitanci a kasar China, kuma suna dab da kammalawa.

A sanarwar da Habibu Nuhu Kila ya fitar tayi nuni da cewa daga cikin Dalibai 160 da aka tura zuwa kasar Sudan sun kunshi Maza 60 da kuma Mata 100.

Kazalika, Gwamna Badaru Abubakar ya shawarci daliban su kasance Jakadu nagari a lokacin da suke karatu a wuraren da aka tura su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: