Dalilan da yasa ake tuhumar DCP Abba Kyari da karbar rashawa

0 76

Fitaccen dan sanda Abba Kyari, wanda aka ambata a matsayin wanda ya ci gajiyar wata damfara ta kasa da kasa, ya bayyana matsayinsa.

Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya ambaci Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, da karbar wani bangare na kudin damfara da ake tuhumarsa a Amurka.

Hushpuppi, wanda ya amince ya amsa laifinsa na damfarar, ya fadawa masu gabatar da kara na Amurka cewa ya bai wa Abba Kyari wani bangare na kudaden laifin da  ya aikata.

Ya ce ya taba sanya Kyari ya kama daya daga cikin abokan sana’arsa na Najeriya lokacin da suka samu sabani.

Abba Kyari ya je shafinsa na Facebook ya tabbatar da matsayarsa dangane da batun.

A bayanan nasa, Abba Kyari ya ce bai nemi wani kudi daga Hushpuppi ba. Amma, ya ce ya gabatar da wanda ake zargin ga mai sayar da hula, wanda Hushpuppi ya biya kusan naira dubu 300.

Leave a Reply

%d bloggers like this: