Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce idan gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle ya sauya sheka zuwa APC mai mulki to zai sauka daga mukamunsa na gwamna.

Shugaban Jam’iyyar PDP Uche Secondus ne ya bayyana haka ga manema labarai, cikin wani hoto mai motsi da PDP ta saka a shafinta na Facebook.

Secondus ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, ya yi bayani a fayyace kan yadda za a iya warware wannan dambarwa.

Ya ce “kujerar da aka zaba, an zabi PDP ne ba wani mutum na daban ba, don haka in Matawalle ya bar wannan jam’iyya to za mu nemi dan jam’iyyarmu ya ci gaba da shugabancin Zamfara” in ji Secondus.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: