Dalilan da yasa aka kama shugaban IPOB, Nmadi Kanu

0 115

Babban Atoni-Janar din kasar Najeriya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata. Bayanai sun yi nuni da cewa an kama shi ne a kasar waje.

A cewar Malami, an yi nasarar cafke shi ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaron Najeriya.

A shekarar 2017 Kanu ya tsere daga Najeriya bayan da wata babbar kotun tarayya ta ba da belinsa bisa dalilai na rashin lafiya.

An gindaya masa wasu sharudda da suka hada da kaucewa yin hira da manema labarai, sharadin da ake zargin ya take.

A shekarar 2019 kotu ta soke belin da ta ba shi.

Gabanin ya fice daga kasar, dakarun Najeriya sun kai wani samame gidansa da ke Afara-Ukwu da ke kusa da garin Umuahia a jihar Abia, inda tun daga lokacin ba a kara jin duriyarsa ba sai a kasar waje.

Ana tuhumar Kanu ne da laifuka 11 da suka shafi cin amanar kasa da jagorantar kungiyar IPOB da ke ta da zaune tsaye hade da mallakar makamai.

A shekarar 2017 hukumomin Najeriya suka haramta kungiyar ta IPOB tare da saka ta cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda saboda fito-na-fito da suke yi da jami’an tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: