Gwamnatin Tarayya ta sake dage ranar rufe aikin hade layukan waya da lambar dan kasa ta NIN zuwa ranar 26 ga watan Yuli, 2021.

Ma’aikatar Sadarwar ta Kasa ce ta sanar da hakan, inda ta cewa zuwa yanzu mutane miliyan 75.3  ne suka  hade lambarsu ta NIN da layukan wayarsu, wadanda kowanne daga cikinsu ke amfani da layuka uku.

Sanarwar da Daraktan Yada Labaranta hukumar Ikechukwu Abinde, ya fitar ta ce, An yanke shawarar ne saboda bukatar hakan da masu ruwa da tsaki suka gabatar, domin a dora a kan nasarar da aka samu bayan bude karin cibiyoyin hada layukan waya da lambar NIN.

A ranar 4 ga watan Mayu, 2021 ne Gwamnatin Tarayya ta kara wa’adin kammala aikin zuwa ranar 30 ga Yuni, domin saukaka wa jama’a samun yin hakan.

Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya yaba da yadda ’yan Najeriya suka rungumi hade layukan wayarsu da lambar NIN.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: