Dalilan da yasa Najeriya zata mika Abba Kyari ya fuskanci shari’ah a kasar Amurka

0 89

Gwamnatin Tarayya ta fara shirin mika dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yansanda, Abba Kyari, domin fuskantar shari’ah a kasar Amurka.

An bayar da rahoton cewa attoni janar na tarraya kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, ya shigar da takardar bukatar hakan a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja, biyo bayan bukatar da wakilin diplomasiyya a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja yayi.

A cewar Abubakar Malami, hukumomin Amurka na bukatar a mika musu Abba Kyari, wanda ake zargi da hannu a wasu laifuka uku.

Attoni janar na tarraya kuma ministan shari’an ya fada cikin takardar bukatar da ya mika cewa ya gamsu da cewa laifukan da ake neman Abba Kyari ya mika wuya basu da alaka da siyasa ko bita da kulli.

Sawaba ta bayar da rahoton yadda gwamnatin Amurka a watan Yulin bara ta ambaci sunan Abba Kyari a cikin abokan huldar Ramon Abbas, da aka fi sani da Hushpuppi, cikin wata badakalar miliyoyin daloli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: