Labarai

Gwamnatin Jihar Neja tace akalla yan bindiga 200 jami’an tsaro suka kashe a hare haren da suka kaddamar a cikin kwanaki 3

Gwamnatin Jihar Neja dake Najeriya tace akalla Yan bindiga 200 jami’an tsaro suka kashe a hare haren da suka kaddamar a cikin kwanaki 3 da suka gabata da zummar karkade su daga jihar.

Kwamishinan tsaro da kananan hukumomi Emmanuel Umar ya shaidawa manema labarai a Minna cewar daga cikin wadanda aka kashe harda kwamandodin kungiyoyin Yan bindigar da suka addabi jihar da suke sansanonin Ali Kawajo da Yello Janbros da Kachalla Halilu da kuma Bello Turji.

Umar yace jami’an tsaron sun yi nasarar kama babura sama da 60 da tarin shanu da kuma makamai daga hannun Yan ta’addan.

Jihar Neja na daya daga cikin jihohin da Yan ta’adda suka hana jama’a zaman lafiya wajen kai munanan hae hare suna kasha jama’a da sace dukiyar su tare da garkuwa da wasu domin karbar kudin fansa.

Daga cikin irin hare haren da Yan bindigar ke kaiwa harda sace daliban makarantar Islamiyar Tegina, matsalar da ta girgiza jama’ar jihar da kuma Najeriya baki daya.

To an gaida Zaliha Muhammad Ahmad da ta karanto mana labaran duniya.

Yanzu kuma sai rahotanni, inda za mu fara da batun rasha da Ukraine ta inda lamarin ya shafi ‘yan Nigeria mazauna kasar;

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: