A karon farko Rasha ta bayyana cewa kusan sojojinta 500 aka kashe a yakin da take yi da Ukraine

0 62

A karon farko Rasha ta bayyana cewa, kusan sojojinta 500 aka kashe a yakin da take yi da Ukraine, yayin da take ci gaba da shan matsin lamba daga kasashen duniya domin ganin ta gaggauta kawo karshen hare-harenta a kasar.

Sanarwar na zuwa ne bayan mako guda da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi shelar kaddamar da luguden wuta akan makwabciyarsu Ukraine.

Mai Magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Rasha, Igor Konashenkov ya ce, baya ga sojojinsu 498 da suka mutu a fagen-daga, akwai karin sojoji dubu 1 da 597 da suka samu raunuka a wannan yakin da suke yi da Ukraine.

Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da Ukraine ta fitar, inda ta yi ikirarin cewa, Rasha ta yi asarar sojojin da yawunsu ya zarta dubu 5 da 700, sannan ta ce, ta kuma  kama kimanin sojojin Rasha 200 a matsayin fursunonin yaki.

 Gwamnatin  Rasha ta tilasta wa wasu mutane shiga cikin wannan yakin bayan ta yi musu rajistan dole a matsayin sabbin sojojin kasar, amma Ma’aikatar Tsaron kasar ta ce, sam al’amarin ba haka yake ba.

Ukraine ta ce, sama da fararen hularta 350 ne aka kashe tu bayan fara yakin a ranar Alhamis da ta gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: