Gwamnatin Tarayya ta sake kafa wata tawaga domin duba yarjejeniyar shekarar 2009 da ta kulla tsakaninta da ASUU

0 96

Gwamnatin Tarayya ta sake kafa wata tawaga domin sake tattaunawa akan yarjejeniyar shekarar 2009 da ta kulla tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU).

Da yake sake kafa tawagar, ministan ilimi, Adamu Adamu, yace akwai bukatar a gaggauta shawo kan dukkan matsalolin da ke cikin yarjejeniyar shekarar 2009.

Hakan, a cewar ministan, yana bisa turba wajen cimma zaman lafiyar da ake bukata a jami’o’in kasarnan.

Adamu Adamu ya sanar da haka yau a Abuja cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar, Ben Goong, ya fitar.

Ya bayyana cewa shugaban tawagar sake tattaunawa akan yarjejeniyar shekarar 2009 da kungiyar ASUU shine Farfesa Nimi Briggs, wanda kuma shine uba a Jami’ar Tarayya ta Alex Ekwueme.

Ministan ya kara da cewa za a kaddamar da tawagar a ranar Litinin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: