Labarai

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sama da mutane miliyan dubu daya ne suke fuskantar barazanar rasa jinsu saboda tsawaita karar kade-kade

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce sama da mutane miliyan dubu daya ne, masu shekaru 12 zuwa 35, suke fuskantar barazanar rasa jinsu saboda tsawaita karar kade-kade da ya wuce gona da iri.

WHO ta bayar da gargadin a cikin wani sabon rahoton shawarwarin kare lafiyar duniya da ta fitar a jiya don magance karuwar barazanar rashin ji.

An kaddamar da sabon tsarin lafiyar kunne a wuraren kade-kade gabanin Ranar Ji ta Duniya, wadda za a yi bikinta a yau.

Sama da mutane miliyan dubu 1 da rabi ne a duniya suke fama da rashin ji, kuma bisa ga alkaluman baya-bayan nan wannan adadin zai iya haura sama da miliyan dubu 2 da rabi nan da shekarar 2030.

WHO ta yi kiyasin cewa za a iya kare rabin mutanen da zasu rasa jin su ta hanyar matakan kiwon lafiyar al’umma.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: