‘Yan majalisar wakilai sun yi watsi da kudirin dokar da ke neman hana jami’an gwamnati tura ‘ya’yansu makarantun kasashen waje

0 68

‘Yan majalisar wakilai a yau sun yi watsi da kudirin dokar da ke neman hana jami’an gwamnati tura ‘ya’yansu makarantun kasashen ketare.

Sergius Ogun na jam’iyyar PDP daga jihar Edo ne ya dauki nauyin kudirin dokar.

A yayin muhawara a zauren majalisar na yau, wasu daga cikin ‘yan majalisar sun dage kan cewa kudirin ya saba wa muhimman hakkokin ‘yan Najeriya.

Wasu kuma sun ce wasu jami’an gwamnati ba sa da hannu wajen sarrafa dukiyar jama’a don haka bai kamata a hana su baiwa ‘ya’yansu ilimi mafi inganci ba.

A baya Sergius Ogun ya dauki nauyin kudirin doka da ke neman a hana jami’an gwamnati amfani da kudaden gwamnati wajen neman magani a kasashen ketare.

Kudirin wanda tuni ya tsallake karatu na biyu yana neman gyara sashi na 46 na dokar kula da lafiya ta shekarar 2014, ta hanyar sanya tarar naira miliyan 500 ko kuma daurin shekaru bakwai a gidan yari saboda amfani da kudaden gwamnati wajan neman lafiya a kasashen waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: