Daraktoci da ma’aikatan ma’aikatunsu su kara kokari wajen gudanar da aiyukansu – Dr. Danzomo

0 272

Kwamishinan Ilmi matakin farko na jihar Jigawa , Dr Lawan Yunusa Danzomo ya bukaci daraktoci da maaikatan maaikatarsa dasu kara kokari wajen gudanar da aiyukansu domin cigaban ilmi

Dr Lawan Yunusa Danzomo yayi wannan kiran a lokacin taro da Daraktoci da  kuma mataimakan daraktoci na maaikatar

Yace a matsayin sabuwar maaikatar Ilmi matakin farko da wannan gwamnati ta kirkiro akwai bukatar kara jajircewa domin marawa kudirin gwamnati baya na cimma manufarta na cigaban ilmi

Dr Lawan Yunusa Danzomo ya shawarci maaikatan dasu yi aiki tare domin cigaban ilmi matakin farko a jihar nan

Yace kofarsa a bude take wajen karbar duk wata shawara da zata kawo cigaban ilimi a jihar nan

A jawabinsa babban sakataren maaikatar , Alhaji Isiyaku S. Shehu ya bukaci maaikatan dasu mara baya ga kwamishinan  domin samun saukin gudanar da aiyukansa

A jawabansu daban daban Daraktocin maaikatar sun yabawa kwamishinan bisa jagoranci na kwarai da yake gudanarwa a maaikatar

Leave a Reply

%d bloggers like this: