Hukumar STOWA ta kashe kudi naira miliyan dubu daya da miliyan dari da sittin a Jihar Jigawa

0 169

Hukumar Samarda Ruwan sha a matsakaitan garuruwa ta jihar Jigawa STOWA tace ta kashe kudi naira miliyan dubu daya da miliyan dari da sittin da hudu wajen gudanar da aiyukan samarda ruwansha a matsakaitan garuruwa daga hawan wannan gwamnati zuwa yanzu.

Manajan Daraktan Hukumar,  Injiniya Adamu Garba ya sanar da hakan ta cikin shirin gidan radio FM Andaza na musamman

Yace aiyukan da hukumar ta gudanar sun hadar da gyaran gidajen ruwa a garuruwa 157 kan kudi naira miliyan 460 da mayar da wasu gidajen ruwa masu amfani da iskar gas zuwa masu amfani da hasken rana guda  33 kan kudi naira miliyan  340, da aikin gina sabbin gidajen ruwa masu amfani da hasken rana a mazabu 14 kan kudi naira miliyan 342 karkashin aiyukan mazabu

Injiniya Adamu Garba ya kara da cewar an gudanar da aiyukan ne a kwarya kwaryan kasafin kudi da gwamnatin jiha ta yi a 2023

Ya na mai cewar a duk shekara hukumar tana kashe kudi naira miliyan dubu biyu wajen gudanar da aiyukan samarda ruwan sha a matsakaitan garuruwa na jihar Jigawa

Manajan Daraktan na STOWA ya ta’allaka nasarorin da hukumar ta samu akan hadin kai da goyan bayan maaikatan hukumar

A cewarsa hukuma ta yi tanadi a kasafin kudi domin aiwatar da aiyukan samarda ruwansha a matsakaitan garuruwa na jihar Jigawa Ya bukaci alumma dasu rinka kula da kayayyakin samarda ruwan sha da aka samar a yankunan su domin gudun lalacewa

Leave a Reply

%d bloggers like this: