Gwamnatin jihar Kano ta fara biyan diyyar Naira Biliyan talatin na rusau

0 182

Gwamnatin jihar Kano ta soma biyan diyyar naira biliyan talatin na rusau da tayi ga masu shagunan masallacin idi dake birini jihar.

Masu shagunan karkashin kungiyar mamallakn shagunan masallacin idi, sun maka gwamnatin jihar a wata Babbar kotu dake Abuja, karkashin mai shari’a Iyang Okwo akan rusa musu kadarorin nasa.

Kotun bayan ta saurari kowane bangare ta kuma yi nazari nakan barnar da akayi musu, ta yanke hukuncin biyan masu shagunan diyyar naira Biliyan 30. Da yake jawabi a wani taron manema labarai, lauyan kungiyar Ma’aruf Yakasai, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta biya naira biliyan daya a cikin naira biliyan 30.

Leave a Reply

%d bloggers like this: