Kafin karshen watan nan za’a kammala gwajin hako ganga dubu sittin a matatar mai ta garin fatakwal

0 253

Kamfanin mai na kasa NNPC ya sanar da cewa kafin karshen watan nan za’a kammala gwajin hako ganga dubu sittin a matatar mai ta garin fatakwal.

Mai magana da yawun kamfanin Femi Soneye, yace  za’a kammala gwajin nan bada jimawa ba domin tabbattar da cewa matatar ta fara aiki yadda ya kamata.

Matatar wadda yanzu haka take a matakin gyara, an tsara zata rika hako ganga dubu sittin a kowace rana.

Duk dai cikin wannan shekara, kamfanin na NNPC ya kuma tsara yadda za’a kara yawan gangar da za’a iya hakowa zuwa dubu 210 a kowace rana. Matatar Mai ta garin fatakwal na daya daga cikin matatun mai  mallakin kasar nan da suka kasance garkame na tsawon lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: