Gwamnatin taraya ta saki kudi Naira Bilyan 50 domin kammala wasu ayyuka a Abuja

0 252

Ministan babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, yace gwamnatin taraya ta saki kudi Naira Bilyan 50 daga cikin kwarkwayar kasafin kudin babban Birnin tarayya Abuja domin kammala wasu ayyuka da ake gudanarwa yanzu haka.

Ministan ya bayyana haka ne a jiya, yayin duba wasu ayyuka a babban Birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana shirin ma’aikatar sa na hada kai da hukumomin tsaro domin saka Kamarori a babban Birnin tarayya domin tabbatar da tsaro. A karshen shekarar 2023 ne, hadakar majalisar dokokin tarayya ta amince da kudi naira bilyan 61. Da miliyan  555 a matsayin kwarkwaryar kasafin kudin babban Birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: