Daruruwan Mambobin APC a Gada, Sokoto Sun Sauya Sheka Zuwa ADC, Sun Danganta Matakin da Rashin Tsaro da Talauci

0 383

Ɗaruruwan mambobin jam’iyyar APC mai mulki a ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto sun fice daga jam’iyyar, sun koma jam’iyyar ADC, suna danganta dalilinsu da tsananin rashin tsaro, talauci da kuma gazawar gwamnati.

A jiya Lahadi aka karɓe su a hukumance ta hannun Sanata Abubakar Gada, babban jigo a tafiyar haɗin gwiwar ADC, wanda ya bayyana wannan mataki a matsayin alamar ƙarin gajiya da fushin jama’a ga gwamnatin APC.

Ya bayyana cewa yawan masu sauya sheka zuwa ADC ba kawai nuna rashin gamsuwa da aikin APC ba ne, har ila yau shaida ce ta shirye-shiryen jama’a na mara baya ga wata sabuwar hanya.

Leave a Reply