Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada cewa dokar da ta kafa tun a shekarar 2013 kan hana aikin Acaba a wasu yankunan birnin Kano tana nan daram, kuma za a ci gaba da aiwatar da ita ba tare da sassauci ba, domin kula da tsaro da rage laifuka.
Wannan na cikin sanarwar da Abubakar Tijjani Ibrahim, mai taimaka wa Kwamishinan Shari’a kan yada labarai, ya fitar a ranar Litinin, 1 ga Disamba, 2025.
A cewar sanarwar, dokar ta haramta zirga-zirgar Acaba a cikin kananan hukumomi Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa, Tarauni, Ungogo, Dawakin Kudu, Fagge da Kumbotso.
Sanarwar ta yi nuni da cewa duk wanda aka samu yana gudanar da aikin Acaba a cikin wadannan yankuna zai iya fuskantar hukunci, ciki har da daurin wata shida, tara naira dubu goma, ko a kwace babur ɗin gaba ɗaya.
A cewar Ma’aikatar Shari’a, a yankunan da aka amince da su, masu babur na bukatar su yi rajista da Mai Anguwa, sashen ayyuka na karamar hukuma da kuma ’yan sandan yankin, domin sauƙaƙa tantancewa da kuma inganta tsaro.
Sanarwar ta kara da cewa an umurci jami’an tsaro su tsaurara bincike da aiwatar da dokar, tare da kara sa ido, domin tabbatar da zaman lafiya da dakile aikata laifuka a cikin jihar.