Dawowar Satar Mutane: Manoma Sun Shiga Fargaba A Taraba

0 54

Dawowar satar mutane: Manoma sun shiga fargaba a Taraba

Manoma a wasu yankunan Jihar Taraba sun shiga fargaba sakamakon sake ɓullowar masu garkuwa da mutane a yankunan karkara.

Rahotanni sun nuna cewa a ’yan kwanakin nan masu garkuwa da mutanen sun kai hare-hare a wasu sassan ƙananan hukumomin Ardo-Kola da Lau, inda suka yi garkuwa da wasu manoma.

Binciken Aminiya ya gano cewa a Ƙaramar Hukumar Lau an yi garkuwa da manoma sama da shida, yayin da a garin Kwando da ke Ƙaramar Hukumar Ardo-Kola ma aka sace wasu manoma, sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba.

Sake ɓullowar lamarin, bayan kusan shekara uku da yankunan suka samu kwanciyar hankali daga matsalar garkuwa da mutane, ya jefa manoma da sauran al’ummar yankin cikin fargaba.

Wani manomi, Jafaru Lawal, daga Ƙaramar Hukumar Lau ya shaida wa Aminiya cewa a makon da ya gabata masu garkuwa da mutane sun sace wasu manoma tare da kashe mutum guda a yankin.

Ya ce yanzu manoma na tsoron komawa gonakinsu saboda gudun kada su sake fuskantar matsalar tsaron da yankin ya sha fama da ita a shekarun baya.

“Manoma, musamman waɗanda gonakinsu ke da nisa da gari, na tsoron zuwa aiki saboda gudun faɗawa hannun masu garkuwa da mutane,” in ji shi.

Jafaru ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Taraba da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin daƙile matsalar, ta yadda manoma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na noma da kasuwanci cikin kwanciyar hankali.

A Ƙaramar Hukumar Ardo-Kola ma, mazauna yankin sun ce manoma na komawa gida tun kafin faɗuwar rana saboda tsoron hare-haren masu garkuwa da mutane.

Wata manomiya mai suna Madam Lami James ta ce a bana amfanin gona ya yi kyau kuma manoma na dab da fara girbi, amma ɓullowar masu garkuwa da mutane ta jefa su cikin damuwa.

Ta ce manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron kada a yi garkuwa da su.

Madam Lami ta tuna cewa a shekarun baya masu garkuwa da mutane sun addabi yankin, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama barin gidajensu da gonakinsu na wani lokaci.

A cewarta, haɗin gwiwar ’yan banga da mafarauta ne ya taimaka wajen fatattakar masu garkuwa da mutanen a wancan lokaci, har aka samu zaman lafiya.

Ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Taraba, jami’an tsaro, ’yan banga da mafarauta da su sake haɗa kai domin daƙile matsalar kafin ta ƙara ƙamari.

Kokarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Taraba bai yi nasara ba, domin kakakinta, ASP Victor Mshelizah, bai amsa kiran wakilin Aminiya ba har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoto.

Leave A Reply

Your email address will not be published.