EFCC Ta Cafke Wani Da Ke Ikirarin Shi Hadimin Shugaban Ƙasa Ne bisa Zargin Damfarar Naira Miliyan 25

0 193

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta gurfanar da wani mutum mai suna Igoin Tokoni Peter a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin damfarar sama da naira miliyan 25.

Ana zargin Peter da bayyana kansa a matsayin mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan bunƙasa fasahar sadarwa da kirkire-kirkire na zamani domin karɓar kuɗi daga wasu kamfanoni da sunan samar musu lasisin harkokin musayar kuɗaɗen crypto.

EFCC ta ce wanda ake zargin ya karɓi kuɗaɗen ne ta hanyar yaudara tsakanin shekarar 2024 da 2025.

Sai dai Peter ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya ba shi beli na naira miliyan 400 tare da sharudda masu tsauri, sannan ya umarci a tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje har sai ya cika sharuddan belin.

Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga Yuli, 2026 domin fara shari’a.

Leave a Reply