Farashin biredi na daya daga cikin kayan abinci da zai tashi saboda rikikkin Rasha da Ukrane

0 75

Farashin biredi, daya daga cikin kayan abinci da ake ci a galibin gidajen kasarnan, na shirin tashi idan rikicin Rasha da Ukraine ya ci gaba da ta’azzara.

Rasha ita ce kasa ta daya da ta fi fitar da alkama a duniya, kuma tana fitar da fiye da kashi 18 cikin 100 na alkama a duniya.

1 Daga cikin matsalolin yakin shi ne, idan har aka hana fitar da kayayyaki daga kasar Rasha, Najeriya za ta iya fuskantar karin hauhawar farashin alkama a kasuwannin cikin gida, sakamakon gibin kayan da za a samu, wanda hakan na iya haifar da karin farashin wasu kayayyakin da ake sarrafawa da alkama, kamar biredi da abincin alkama da sauransu.

A cewar babban bankin kasa (CBN), alkama ita ce kayan abinci na uku da aka fi amfani da shi a kasarnan, kuma ana noma kashi 1 cikin 100 kacal na ton miliyan 5 zuwa 6 na alkamar da ake amfani da ita a duk shekara.

Inda kasar ke dogaro kan shigo da ita daga kasashen waje domin biyan bukatun cikin gida.

Har ila yau, Najeriya na shigo da nau’o’in abincin ruwa daga kasar Rasha, wasu daga cikinsu sun hada da nama, da kifin gwangwani da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: