Farfesa Yemi Osinbanjo yace daga yanzu za’ana tsaurara binciken kudade a ma’aikatu da hukumomin gwamnati dake fadin kasar nan

0 78

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo yace, daga yanzu za’ana tsaurara binciken kudade a ma’aikatu da hukumomin gwamnati dake fadin kasar nan.

Ya kara da cewa zai taimakwa wajan gano bata da gari, da kuma marasa gaskiya a cikin gwamnati, domin farfado da tattalin arziki da kuma inganta ayyuka a fadin kasar nan.

Babban mai taimakwa mataimakin shugaban kasa a kafafen yada labarai Loalu Akande ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa daya fitar a babban birnin tarayya Abuja.

A cewar sa mataiamakin shugaban kasa ya bayyana hakan ne a wurin taron rufe kasuwanci na shugaban kasa karo na 5 da aka gudanar.

Taron da aka gudanar a jiya da dare a babban dakin taro na fadar shugaban kasa dake abuja.

Cikin manyan bakin da suka halarci taron sunhada shugaban kwamitin kafafen yada labarai na majalissar dattawa Ajibola Basiru, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da kuma ministan yada labarai na kasa Lai Mohammed.

Sauran sunhada da minsitan tama da karafa Olamilekan Adegbite, Karamin ministan kudi kasafi da tsare tsatre na kasa Clem Agba sai kuma Karamin minsitan lafiya Olorunnimbe Mamora da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: