Fargaba:Babbar illar Da Cutar Corona Virus Zata Yiwa Nijeriya

0 109

Kasar Najeriya zata iya fuskantar karancin magunguna sakamakon dakatar da shigo da magunguna da kasar india tayi zuwa kasar nan da wasu kasashen da ke fadin duniya.

Babbar daraktar hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa Mojisola Adeyeye tace Najeriya na cikin barazanar fuskantar karancin magunguna saboda dogara da kasar nan tayi da samun magunguna daga wasu kasashen na kashi 70 cikin dari na magungunan da ake amfani da su ana shigowa da su ne daga wasu kasashen.

 Ta kara da cewa kasar India wacce ta kasance wajan samar da maguguna da yafi na ko ina a fadin duniya ta sanya tsaro akan magungunan ta, kasancewar yawancin abubuwan da take hada magunguna da su ana shigowa da su ne daga kasar Chaina.

Ta bayyana cewa akwai bukatar a tabbatar ana samar da magunguna na cikin gida, saboda barazanar karancin magunguna da ka iya shafar kasar nan idan har cutar COVID-19 ta cigaba da bulla.

Leave a Reply

%d bloggers like this: